3 Janairu 2022 - 16:41
​An Bayar Da Hutu A Wasu Jihohin Iraki A Ranar Tunawa Da Shahadar Qassem Sulaimani Da Abu Mhadi Muhandis

Wasu daga cikin jihohin kasar Iraki sun bayar da hutu domin tunawa da zagayowar ranar shahadar janar Qassem Sulaimani da Abu Mahdi Almuhandis.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - An dai gudanar da irin wannan taro a birane daban-daban na Iraki da suka hada da birnin Bagadaza fadar mulkin kasar ta Iraki, inda mutane kimanin miliyan uku suka halarci gangamin, wanda ba a taba ganin makamancinsa a birnin ba.

Babban kwanadan dakarun sa kai na kasar Iraki Faleh Fayyad ya gabatar da jawabia wurin, inda ya jaddada wajabcin ficewar sojojin Amurka daga kasar Iraki a daidai wa'adin da aka diba musu, inda ya ce babu wani sassauci kan wanna matsayar da al'ummar Iraki suka dauka.

Baya ga birnin Bagadaza, an gudanar da irin wannan gangamia wasu biranen, da suka hada da Najaf, Karbala da sauransu, inda malamai da jami'ai da sauran dubban al'ummar gari suka halarta.

342/